DARASIN RAYUWA: Wasu matasa biyu sun salwanta da rayuwar su domin neman duniya.

Wadannan matasa an kamasu da laifin cire al'aurar wata yarinya karama domin suyi tsafi da shi suyi kudi

'Yan sanda sun kamasu, bayan kammala bincike an kaisu Kotu, Kotu ta tabbatar da laifin da suka aikata, kuma ta yanke musu hukuncin shekaru 70 a gidan yari

Abdulkadir Wada yana da shekaru 19
Adamu Abdulra'uf yana da shekaru 20

Abdulkadir zai kammala zaman gidan yari yana da shekaru 89
Adamu zai kammala zaman gidan yari yana da shekaru 90

Ku fahimci darasin rayuwa anan, gasu nan yarane matasa balagar fari, rashin hakuri yasa ba zasu mori rayuwar duniya ba

Zasu tsufa a gidan yari babu karatu, babu aure balle su haihu, shikenan rayuwar ta kare a cikin da na sani marar amfani

Malamai sun fada mana cewa, duk wanda ya nemi kudi ta mummunan hanya da zai yi hakuri ya dogara ga Allah zai samu kudin ta hanya mai kyau

Sai dai illar samun kudi ta mummunan hanya shine ba zaka taba jin dadin kudin ba ko da ka samu, wani lokacin ma idan kayi yunkurin neman kudi ta mummunan hanya sai asirinka ya tonu, kamar yadda ya faru da wannan yara

Muna fatan Allah Ya tsare mana imanin mu, Ya bamu halal ya nesanta haram daga garemu

Comments

Popular posts from this blog

OUR HOPE ALHAJI ATIKU ABUBAKAR 2027

ELECTORAL ACT: ADC ACCUSES SENATE, HOUSE OF DELAY TACTICS

PRESS STATEMENTADC Condemns Attempted Arrest of Mallam Nasir El-Rufai, Warns Against Escalating Pattern of Political Intimidation