Matasan Jam'iyyar PDP Sun Fara Shirye-Shiryen gangamin taron Dalibai Da Matasa a fadin kasar nan/Taron wayar da kai.

Yarima Muhammad Kadade shugaban matasan jam'iyyar PDP ta kasa da mataimakin sa Hon. Timothy Osadolo sun  tattaro kan Matasan Najeriya Domin taron wayar dakai gameda zabin Atiku da Okowa. 

A ranar Asabar ne ake sa ran kungiyyar kamfen din matasan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP-YCC) za ta fara taron ta na Matasa da Dalibai masu ruwa da tsaki a cikin shiyyoyin siyasar kasa guda shida domin wayar da kan matasan Najeriya domin su marawa takarar Alhaji Atiku Abubakar, da Dr Ifeanyi Okowa. ‘Yan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar. Tawagar matasan karamar hukumar da ake sa ran za ta fara aiki a shiyyar Arewa maso Gabas, za ta kasance karkashin jagorancin daraktan wayar da kan matasa na jam’iyyar PDP-YCC kuma shugaban matasan jam’iyyar na kasa Hon. Muhammad Kadade. Haka kuma a cikin tawagar akwai mataimakin daraktan wayar da kan matasa kuma mataimakin shugaban matasa na kasa Hon. Timothy Osadolo, da sauran shugabannin matasan jam'iyyar. 

Comments

Popular posts from this blog

OUR HOPE ALHAJI ATIKU ABUBAKAR 2027

ELECTORAL ACT: ADC ACCUSES SENATE, HOUSE OF DELAY TACTICS

PRESS STATEMENTADC Condemns Attempted Arrest of Mallam Nasir El-Rufai, Warns Against Escalating Pattern of Political Intimidation