Ɗan takarar majalisar dokokin jiha mai wakiltar mazaɓar Kurfi ya gana da matasan Kurfi.

Dan takarar kujerar majalisar dokokin jiha mai wakiltar mazaɓar Kurfi, Hon. Abdullahi Muhammad (Dan-Maliki), a jiya, 28 ga watan Janairun shekarar 2023, ya samu ganawa da matasa da kuma shuwagabannin dalibai a ƙaramar hukumar Kurfi ta jihar Katsina.

Shugaban matasan ya tabbatar da cewa matasa da kuma ɗaliban ƙaramar hukumar Kurfi basu san wata jam'iyyar da ta wuce PDP ba kuma a shirye suke domin tabbatar da sun yi dandazo a ranakun zaɓuka masu zuwa domin zaɓen jam'iyyar PDP a dukkan matakai.

Shi ma jagoran jam'iyyar PDP na ƙaramar hukumar Kurfi, Amadu Mainasara, a nasan jawabin, ya tabbatar da cewa al'ummar karamar hukumar Kurfi basu san wata jam'iyyar siyasa sama da PDP ba kuma ya tabbatar da cewa a shirye suke domin bawa jam'iyyar cikakken goyon baya a zaɓe mai zuwa.

Mai sanarwa:
Yasir Ibrahim Jami'in hulɗa da jama'a na Jihar Katsina
(Daga sashen yaɗa labarai.) Ƙwamatin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyar PDP na ƙasa

Comments

Popular posts from this blog

OUR HOPE ALHAJI ATIKU ABUBAKAR 2027

ELECTORAL ACT: ADC ACCUSES SENATE, HOUSE OF DELAY TACTICS

PRESS STATEMENTADC Condemns Attempted Arrest of Mallam Nasir El-Rufai, Warns Against Escalating Pattern of Political Intimidation