2023: RUKAYYA ATIKU ABUBAKAR TA SAUƘA A GARIN BAUCHI ... DOMIN NEMAWA MIJIN TA MAGOYA BAYAN AL'UMMA
Matar tsohon mataimakin shugaban ƙasar kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyar PDP Atiku Abubakar a babban zaɓen 2023 , Rukayya Atiku Abubakar tare da yan ƙwamatin ta na yaƙin neman zaɓe (PRACO) , yanzu haka sun sauƙa a garin Bauchi domin ƙira ga matan yankin arewa maso gabas su goyawa mijin ta baya a zaɓen dake tafe.
Wannan dadine akan ayyukan da take tun farkon fara yaƙin zaɓe.
Kwana nan, Mai girma, Rukayya ta haɗa taru kan ganawa da mata a yanku nan dake ƙasar nan , a wani shiri da take na tattaunawa da mata tare wayar musu dakai akan manufofin maigidan ta , Atiku Abubakar don su fahimci shirin da yake dashi akan mata musamman akan matsalolin da suka musu katutu idan an zaɓe sa shugaban ƙasar Najeriya a 2023.
Yayin wata Shira da tayi, Rukayya tace mijina, Atiku Abubakar shine ɗan takarar da yake da niyyar damawa da mata da matasa a cikin gwamnatinsa, dalilin hakan yayi alƙawarin samar da $10 biliyan domin bawa matasa maza da mata jari ".
A wani taro data gudanar a yankin arewa maso yamma Rukayya ta bayyana dukkan manufofin maigidan ta, inda tayi ƙira ga dukkan matan dake yankin arewa maso yamma dasu zaɓe PDP a babban zaɓen dake tafe 2023 .
Bayan wannan ziyarorin da Rukayya take, kowa yasan Rukayya a shirye take ta yaɗa dukkan manufofin PDP ga mata da sauran yan Najeriya , a shirye shiryen da muke na ganin an dama dasu a cikin gwamnati da zarar mijinta ya zama shugaban ƙasa a zaɓen dake tafe .
Sanarwa:
Ƙwamaatin yaɗa labarai na PRACO
Comments
Post a Comment