Abun Al'ajabi
Wuta taƙi cin itacen dake ɗauke da sunan Annabi MUHAMMADU SAW ♥️
Wani abun al'ajabi ya faru a karamar hukumar Funakaye cikin Jihar Gombe cikin garin Bajoga, unguwar Sabon layi.
Wadan nan hotunan da kuke gani da idanun ku, wani abun al'ajabine ya faru a gidan Burodi na "BABANDU BAKERY", Inda wani Itacen wuta ya kwana yanaci da wuta a dakin gasa Burodi, amma wani bangaren Itacen baici wutar ba, daga baya ake gane cewa akwai sunan MANZON ALLAH (S.A.W) a jiki kamar yadda kuke kallo a cikin hotunan nan da suke tare da wannan rubutu.
Allah ya kara mana Imani, ya bamu ikon kara kare martabar MANZON ALLAH (S.A.W), ya bamu ikon koyi da halayen shi, da dabi'un shi, ya Sanya mu a cikin ceton shi.
.
صلي الله عليه وسلم
Comments
Post a Comment