Siyasar Najeriya, Dole mu koma ga faɗin Allah (SWA) Acikin Suratul Baqra Aya ta 216.
Wato magana ta gaskiya dole mu koma ga Allah kachokam domin Allah SWA acikin Suratul Baqra Aya ta 216, yace "A gareku an rubuta yaƙi sai dai cewa ya kasance abin ki ne a gare ku...". Har yanzu acikin ayar Allah yace, "da sannu zaku ki wani abu kuma alkhairi ne a gare ku, kuma da sannu zaku so wani abu kuma sharri ne a gare ku, Allah Ya sani ku baku sani ba.
Abinda yasa na kawo wannan ayar shine a zahirin gaskiya duk wani ɗan Najeriya imma bai san wannan ayar tana cikin Al-Qurani ba to yaga aikin ayar a zahiri. Domin ta bayyana mana zahiri Kuru Kuru, ko makaho saida yaji kuma ya ganta.
A lokacin kafin zaɓen shekarar 2015 Shugaba Buhari bashi da ko sisin kwabo, amma a haka aka zaɓe sa a zaɓen fidda gwani aka bar Alh Atiku Abubakar duk da tarin kuɗaɗen sa. Wannan shine SO da KI irin wanda Allah ya kwatanta mana a cikin waccen Ayar. Kuma fa ku sani a lokacin koda Atiku ya fito a wata jam'iyyar da bam sai mutane sun zaɓi Buhari su bar Atikun domin dai waccan ayar ta tabbata a kan mu. Domin me? domin SO.
Wannan so ɗin ne yazo yazama SHARRI a gare mu baki daya sannan KIN da mukawa Atiku kuwa a cikin rashin sani kila da shine muka zaɓa koda bama so ɗin da sai yazamo alkhairi a gare mu.
Amma yanzu ma muna da sauran sarari domin Allah ya ƙudirta Alh Atiku Abubakar ɗin baice ya fasa tsayawa takarar ba. Wannan karo ma ya fito domin fatan yazamo alkhairi a gare mu da kuma kasar mu.
A domin haka nake kira ga dukkanin al'ummar ƙasa ta Najeriya da mu mara wa Alh Atiku Abubakar baya domin ceto kasar mu Najeriya da yardar Allah.
Kowa zai shede shi cewa shi mai girma Alh Atiku Abubakar baya bukatar komai, domin a yadda yake babu abinda Allah bai masa ba.
Daga karshe ina kira ga daukakin mutane masu hankali da suyi kyakkyawan nazari kuma su sanar da makusantan su cewa mu zaɓi Atiku Abubakar kuma muyi addu'a da fatan Allah yasa shine Alkhairi a garemu baki ɗaya.
Rubuta wa da yaɗawa: Comrade Abdul Auwal Mahdi.
Comments
Post a Comment