Yaushe zamu farga al'ummar Arewa?

 

by: Comrade Auwal Abdul Mahdi

Idan da nine Buhari da sauka zanyi daga kan karagar mulkin nan. Domin komai daya zargi gwamnatin data gabata sai da Allah ya jarabce shi ninki biyu ko uku.
Kama daga matsalar tsaro, hauhawan farashin kayan masarufi, karayar tattalin arzikin kasa, yajin aikin Malaman jami'a, satar dukiyar ƙasa, rashin bin doka da oda dss.
Kazawar Buhari duk duniya sun shaida cewa ya gaza. Amma a haka zaka wasu masu son zuciya daga cikin al'umma suna fadin ai wai halin mu ne har sai mun chanja kafin Allah zai yaye mana wannan musifar da muke ciki.
Idan muka lura da magar za muga tayi kamar wata aya ko hadisi da idan har wani yaja zai iya yin ridda kuma ba haka bane fa! Kurum dai sunayin amfani da ire-iren waɗannan maganganun ne domin su ribaci imanin masu raunin tunani.
Da farko dai ya kamata musan cewa, kasar nan ba mulkin Daular Musulunci muke ba. Balle ace wai ana aiki da shari'ar Muslunci ne wajen aiwatar da dukkan lamari da ya shafi kasar nan.
Inda muna amfani da shari'ar Allah ne kamar yadda ya umarta, to da ba haka zamu kasance ba. Dole asamu daidaito akan dukkan lamari, kuma idan muka shiga rudani Allah zai bamu mafita ko bamu nema ba domin muna bin dokokin Sa.
Amma yanzu, shuwagabannin mu sunce babu ruwan su da lamarin Allah, musamman wannan shugaban kasar da yasa hannu ya tunɓuke duk wani tubali da gwamnatocin baya suka kafa domin taimakon addini yace babu ruwansa da hakan.
Kuma a haka wai sai kaji wani yana bashi kariya ta bangaren addini. Wannan shirme da yawa yake. Wai ko mun mata faɗin da akeyi ne na cewa من كان لله ، كان الله له. Ma'ana: duk wanda yazama na Allah, Allah ma zai zama nashi.
To! Mutum yace babu ruwansa da lamarin Allah taya za'ayi Allah ya shigo lamarin sa shima? Dole mu fadawa kan mu gaskiya. Hatta Malaman da sukayi ruwa sukayi tsaƙi gurin ganin ya samu nasara a zaɓe ta hanyar wa'azi da ayoyin da hadisan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, wasun su sun koka kuma sunyi da sun sani sai kaɗan masu son zuciyar cikin su ne har yanzu basu ganin laifin sa har kwanan gobe.
Wasu daga cikin su sun kasa fitowa su yabe shi ko su kushe shi saboda kila ko suna tsoron zaluncin sa ko kuma tsoron fusatattun al'umma suyi musu bore.
Idan gaskiya ake so dole a saki son zuciya mufadi gaskiya.
Ya kuke ganin idan da Buhari ba musulmi bane kuma ba dan arewa ba? Da wane irin tsinuwa ne da Allah wadai bazai samu ba? Amma saboda munafurci al'ummar mu suna cikin matsi da azaba babu wanda zai iya fitowa yace an an gaza. Idan malami ya daure ya fito yayi magana, idan limamin masallacin gwamnati ne ko na ya'yan ta sai acire shi daga limancin. Munga abinda ya faru da Sheikh Nura Khalid a Abuja.
Yaushe zamu farga al'ummar Arewa?

Comments

Popular posts from this blog

OUR HOPE ALHAJI ATIKU ABUBAKAR 2027

ELECTORAL ACT: ADC ACCUSES SENATE, HOUSE OF DELAY TACTICS

PRESS STATEMENTADC Condemns Attempted Arrest of Mallam Nasir El-Rufai, Warns Against Escalating Pattern of Political Intimidation