Gwala-gwalan tambayoyi 17 ga jam'iyyar haɗaka ta APC.
Ina yan jam'iyyar haɗaka ta APC kuzo ku bamu amsar waɗannan tambayoyin danasa musu suna 17 Golden Questions a turance.
Da Hausa kuma gwala-gwalan tambayoyi 17.
Gasu kamar haka:
1) Da kukayi alkawarin kawo tsaro kun kawo?
2) Da kukayi alkawarin maida Naira daidai da dalla kun mayar?
3) Da kujayi alkawarin samar da wutar lantarki kun samar?
4) Da kukayi alkawarin gyara matatun man fetur kun gyara?
5) Da kukayi alkawarin gina matatun man fetur kun gina?
6) Da kukayi alkawarin tona Dam a Garin Baru Kun tona?
7) Da kukayi alkawarin rage farashin man fetur kun rage?
8) Da kukayi alkawarin inganta ilimi kun inganta?
9) Da kukayi alkawarin inganta lafiya kun inganta?
10) Da kukayi alkawarin inganta noma kun inganta?
11) Da kukayi alkawarin samar da aikin yi ga matasa kun samar?
12) Da kukayi alkawarin zaku rage ɓarnatar da kuɗin ƙasa wajen rage yawace yawace da hidimar banza kun rage?
13) Da kukayi alkawarin Dawo da kamfanin jiragen saman Najeriya (Nigerian Airways) kun dawo dashi?
14) Da kukayi alkawarin hana fita kasar waje domin zuwa asibiti kun hana?
15) Da kukayi alkawarin hana fita karatu kasar waje kun hana fita?
16) Da kukayi alkawarin habbaka kasuwanci kun habbaka?
16) Da kukayi alkawarin tayar da kamfanin karafe dake Ajakuta kun tayar?
17) Da kukayi alkawarin hana satar dukiyar ƙasa kun hana?
Don Allah ba hayaniya nake so ba amsa da hujjoji nake so ga duk wanda yaga zai iya.
Nagode
Naku a har kullum: Comrade Auwal Abdul Mahdi ( a.k.a Mahdizzaman)
Comments
Post a Comment